3 Agusta 2020 - 13:44
Zarif Ya Bukaci A Kara Tsawaita Yarjeniyoyin Tsakanin Rasha Da Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr Javad Zarif ya bayyana cewa akwai bukatar kasar Iran da Rasha su sabonta yarjeniyoyin maso dogon zango a tsakaninsu zuwa lokaci mai tsawo sosai.

ABNA: Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Lahadi a lokacinda yake ganawa da shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin kasar Rasha (DUMA), Leonid Slutsky a nan birnin Tehran.

Jami’an gamnatocin guda biyu sun tattauna batutuwa wadanda suka hada da kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu, yarjejeniyar JCPOA ta kasar Iran, rikicin kasashen Iraqi, Siriya, Libya da Yemen.

Har’ila yau Slutsky ya gana da shugaban majalisar dokokin kasarb Iran Mohammad Baqer Qalibuf a jiya Asabar.

342/